4 Maris 2015 - 06:08
Martanin Zarif akan surutan Natanyahu

A yayin da yake maida martini a kan surutan Benjamin Natanyahu wanda ya gabatar a majalisar dokoki ta Amurka, ministan harkokin kasashen waje na Iran yace, Natanyahu na neman dagula al’amura ne.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti{A.S}-abna-Mahammad Zarif yace, Firaministan haramtacciyar kasar Isra’ila yana neman kawo cikas ne a tattaunawar da ke gudana tsakanin  Jamhuriyar musulunci ta Iran  da kasashen 5+1 dangane da batun makamashin Nukiliya na zaman lafiya.

Tabbas Natanyahu ba zai samu nasara ba a cewar Zarif.ABNA